Syria: Shirin tsagaita wuta ya fara aiki

Dakarun dake biyayya ga Shugaba Assad bayan sun kwato wani yanki na gabashin Aleppo ranar Lahadi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kafin fara aiwatar da yarjejeniyar, bangarorin sun yi ta musayar wuta

Wata yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a Syria, ko da yake babu tabbas a kan ko za a aiwatar da ita yadda ya kamata.

Rundunar sojin kasa ta Syria dai ta ce tana aiwatar da yarjejeniyar wacce ta fara aiki da maraice, amma kungiyoyin 'ya tawaye ba su fito fili sun fadi yadda suke kallon ta ba.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerru, wanda ya taimaka wajen cimma yarjejeniyar, ya yi gargadin cewa wannan ka iya zama dama ta karshe ta samar da zaman lafiya a hadaddiyar kasar Syria.

Kungiyoyin agaji na fatan kai dauki a yankunan da suka fi shiga halin ni-'ya-su, musamman Aleppo birnin da yaki ya daidaita.

Mista Kerry, wanda yake jawabi daga ofishinsa a Washington, ya ce rahotannin farko-farko na nuna cewa fadan ya dan ragu.

Sai dai kuma ya kara da cewa ya yi wuri a yanke huknci a kan tasirin da tsagaita wutar za ta yi.