'Yar Najeriya ta haihu a teku

Mahaifiyar jaririn dai tana kan hanyar tafiay ci rani ne

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto,

An haifi jaririn a tekun Bahar Rum, dan haka ba a yanke hukunci kan kasar sa ba.

Wata 'yar Nigeria dake tafiya cirani zuwa nahiyar turai ta haifi jariri a cikin jirgin ruwan kungiyar likitoci masu bada agaji ta duniya wato MSF a tsakiyar tekun Bahar Rum, jim kadan bayan ceto ta

A da matar dai mai suna Faith Oqunbor tana cikin wani kwale kwalen roba ne mara tsafta, mai cike da jama'a, kafin daga baya a cece ta.

Kungiyar ta MSF tace an haifi jaririn lafiya, sai dai irin wannan haihuwa tana da hadari.

Iyayen jaririn sun rada masa suna Newman Otas, to sai dai da yake an haife shi ne a tekun kasa da kasa, ana takaddama a kan ko shi dan wace kasa ne.

MSF ta ce mutane 392 ne a cikin jirgin dake dauke da 'yan ci ranin, kuma a cikin su akwai mata bakwai masu ciki.

Wata jami'a a kungiyar likitocin da ke bada agaji Alva White tace a watan Mayun da ya gabata ma wata yar Kamaru ta haihu a teku, ko da dai ta ce ba kasafai ake samun irin wannan nakuda a cikin jiragen agaji ba.

A duk shekara dubban mutane na jefa rayuwarsu cikin hadari ta hanyar yunkurin tsallakawa turai daga Libiya.

A bara sama da mutum dubu uku da 700 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon irin wannan tafiya.