Brazil: An tsige shugaban majalisa Eduardo Cunha

Tsohon shugaban majalisar wakilan Brazil Eduardo Cunha
Bayanan hoto,

An tsige Eduardo Cunha ne saboda cin hanci

`Yan majalisar wakilan Barzil sun kada kuri`a da gagarumin rinjaye da ta goyi bayan korar tsohon Kakakin majalisar, Eduardo Cunha, wanda ya yi ruwa-da-tsaki wajen jagorancin tsige tsohuwar shugabar kasar, Dilma Rousseff.

Ana dai zargin Mista Cunha da karbar rashawa ta miliyoyin daloli daga hannun kamfanin mai na Petrobras.

To sai dai Mr Cunha ya musanta cewa ya aikata wani laifi, yace kawai magoya bayan tubabbiyar shugaba Dilam ne ke yi masa bita da kulli suna son daukar fansa, bisa tsigeta da aka yi albarkacin kokarin da ya yi.

A watan Maris din bara Edwardo Cunha ya bayyana cewa bashi da kowane irin asusu a ko ina wanda bai bayyana ba.

To sai dai daga baya hukumomin Switzerland sun bada bayanai ga wata hukuma dake binciken cin hanci da rashawa a Brazil, inda bayanan suka nuna cewa dan majalisar Cunha da mai dakinsa Claudia Cruz suna da wasu asusai na sirri da suke da kudaden da suka kai dala miliyan 5.

Ana yi masa kallon taskar asiran majalisar da ake zargin 'ya'yanta da dama da badakalar cin hanci, kuma ya yi barazanar cewa zai yi bankadar da za ta lankayo wuyan wasu manyan `yan siyasa a kasar.

Wannan mataki da `yan majalisar wakilan Brazil suka dauka ya cire wa Mista Cunha rigar-kariya daga gurfana gaban kuliya, don haka za a iya tsare shi, tare da gurfanar da shi gaban shara`a ba tare da bata lokaci ba.

A watan jiya ne dai Mr. Cunha ya jagoranci tsige tshohuwar shugaba Dilma Rousseff bisa samunta da laifin sauyawa wasu kudade mahalli a cikin kasafin kudi, wanda hakan laifi ne a dokokin Brazil, ko da dai ta bayyana matakin da cewa wani juyin mulki ne.