Sojojin Rasha za su ba da tsaro a Syria yayin tsagaita wuta

Wasu daga cikin mayakan 'yan tawaye a Syria

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Masu sa-ido sun ce galibi an tsagaita wuta

Rahotanni sun ce dakarun Rasha sun hau kan wata muhimmiyar hanyar da ta isa arewacin Syria don bayar da dama a kai kayan agajin da ake matukar bukata yayin tsagaita wuta na wucin-gadi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce lafiyar ma'aikatanta na agaji na gaba da komai, don haka ba za ta kudiri aniyar aikewa da ayarin kayan agaji zuwa Aleppo ba har sai an ba da garantin za a kare su.

Wani wakilin BBC a arewacin Turkiyya--inda ayarin ke jira--ya ce yanzu sojojin Rasha ne za su samar da tsaro, kuma ana sa ran ayari na farko zai dauki hanya ranar Laraba.

Masu sa-ido a cikin kasar Syria sun ce galibi ana aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar, ko da yake an dan yi mata karan-tsaye nan da can.