Syria: Rasha ta yarda a tsawaita yarjejeniya

Dakarun dake biyayya ga Shugaba Assad bayan sun kwato wani yanki na gabashin Aleppo ranar Lahadi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kafin fara aiwatar da yarjejeniyar, bangarorin da ke fada da juna sun yi ta musayar wuta

Rundunar sojin Rasha ta mara baya ga tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar da ita da Amurka suka taimaka aka cimma a Syria.

A cewar kasar ta Rasha shugaban cibiyarta ta sa-ido a kan tsagaita wutar dake Syria zai gana da takwaran aikinsa na Amurka nan gaba a ranar Laraba.

Sa'o'i a48 ke nan tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki; masu sa-ido kuma sun ce babu wani farar hula da ya mutu a wadannan sa'o'i duk da karan tsayen da aka yi wa yarjejeniyar..

Har yanzu Majalisar Dinkin Duniya ba ta samu damar kai kayan agaji ba, musamman a gabashin Aleppo wanda ke hannun 'yan tawaye.

Sai dai kuma an bayar da rahoton cewa dakarun gwamnati da mayakan 'yan tawaye na shirin janyewa daga wata muhimmiyar hanyar zuwa yankin ranar Alhamis.