''Kenya da MDD sun saba ka'ida kan 'yan hijirar Somaliya''

'Yan gudun hijirar Somaliya sun yi curko-curko a kan iyaka
Bayanan hoto,

'Yan gudun hijirar Somaliya sun rasa ta yi

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta soki gwamntin Kenya da kuma hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, kan rufe sansanin 'yan gudun hijirar Somaliya.

Kungiyar ta zarge su da gaza bin ka'idojin kasashen duniya a matakin mayar da 'yan gudun hijirar Somaliyan gida daga sansaninsu na Daadab da ke Kenya.

Darektan kula da hakkin 'yan gudun hijira na kungiyar Bill Frelick, ya ce hukumomin Kenyan, ba su ba wa mutanen da abin ya shafa zabin ko su ci gaba da zama a sansanin ba ko kuma su koma gida.

Sannan kuma ya ce ita hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya a nata bangaren ba ta sheda wa mutanen ainahin yanayin tsaro da ake ciki ba a can Somaliya.

Su dai gwamnatocin kasashen Kenya da Somaliyan sun ce lokaci ya yi da ya kamata a rufe sansanin na Daadab wanda yake kasar Kenya.

Amma kuma, shugabannin yankin Jubaland, inda yawancin 'yan gudun hijirar suke nufa a kwanan nan, sun daina karbar 'yan gudun hijirar, a bisa dalilan cewa ba su da isassun kayan kula da su.

A dangane da hakan ne yanzu 'yan gudun hijirar da dama suka rasa ta yi, ya kasance suna zaune curko-curko a kusa da kan iyakar kasashen biyu.