Gaskiyar rashin lafiyar Hillary Clinton ta fito fili

Hillary Clinton na fama da cutar sanyin hakarkari wato Pneumonia.
Bayanan hoto,

'Yar takarar shugabancin Amurka, a jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton

'Yar takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar, Democrat, Hillary Clinton, ta bayar da cikakkun bayanai kan cutar sanyin hakarkarin da take fama da ita.

Magoya bayan Clinton dai sun ce cutar ba wadda wani zai iya dauka ba ce.

Sannan an dora ta a kan magani na tsawon kwana goma.

Haka kuma likitanta ya ce tana samun sauki sannan kuma tana da koshin lafiyar da za ta iya shuganacin kasar.

Shi ma abokin hamayyarta na jam'iyyar Republican, Donald Trump, a baya-bayan nan ya shelanta cewa likitansa ya fada masa cewa yana bukatar ya rage tebarsa.