'Yan Republican sun amince da mallakar bindiga ba izini

Missouri, governor, Jay Nixon
Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Missouri Jay Nixon na adawa da matakin

'Yan jam'iyyar Republican a jihar Missouri ta Amurka sun kada kuri'a inda suka amince yawancin magidanta su mallaki bindiga ba tare da lalle sai sun bukaci izini ba.

'Yan majailsar sun amince da hakan ne kuwa duk da adawar da aka nuna cewa matakin zai sa a kara samun kisan bakaken fata.

Majalisar wadda 'yan Republican suke da gagarumin rinjaye a cikinta ta kawar da matakin kujerar-nakin da gwamnan jihar Jay Nixon ya dauka kan kudurin.

Maria Chappelle-Nadal daga mazabar Ferguson na cikin 'yan majalisar dattawan da suka yi gargadin cewa matakin zai sa a kara samun yawan bakaken fata da ake kashewa.

A Ferguson din ne aka yi ta tarzoma bayan da wani dan sanda farar fata ya harbe wani matashi bakar fata Michael Brown, shekara biyu da ta wuce.

'Yan Republican din sun ce dokar za ta ba wa 'yan kasa masu kiyayewa da doka damar kare kansu da iyalansu.