Pakistan- Jiragen kasa sun yi karo mutane 4 sun mutu

jirgin kasa, hadari

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Hadarin jiragen kasa

Wani jirgin fasinja da na dakon kaya sun yi taho-mu-gama a yankin tsakiyar kasar Pakistan abin da ya yi sandin mutuwar mutane akalla hudu tare da raunata wasu sama da 100.

Jami'an hukumar jiragen kasa sun ce hatsarin ya auku ne a kusa da birnin Multan na Punjab.

Rahotannin kafofin yada labari na kasar sun ce matukin jirgin dakon, ya tsaya bayan da ya buge wani mutum a kan layin dogon, daga nan ne kuma, sai wani jirgin fasinja da ya nufi Karachi ya yi karo da shi.

Taragwai guda hudu ne suka fadi daga layin dogon a hadarin.