Syria: Jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun fusata

Dakarun dake biyayya ga Shugaba Assad bayan sun kwato wani yanki na gabashin Aleppo ranar Lahadi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kafin fara aiwatar da yarjejeniyar, bangarorin sun yi ta musayar wuta

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun nuna fushi da takaicinsu sakamakon gazawa wajen kai kayan agaji Syria, duk de cewa yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki ranar Litinin.

Wakilin Majalisar na musamman, Staffan de Mistura, ya ce gwamnatin Syria ba ta bayar da takardun izini ba kamar yadda ta yi alkawari.

Sai dai Rasha, babbar mai mara baya ga Shugaba Assad, ta ce dakarun gwamnati sun janye daga muhimmiyar hanyar zuwa birnin Aleppo don samar da dama ga ayarin kayan agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya j yankunan da ke hannun 'yan tawaye ranar Juma'a.

Rundunar sojin Rasha ta ce dakarun gwamnati ka iya komawa wuraren da suka ja daga idan dakarun 'yan tawaye ba su janye daga Hanyar Castello ba.