'Lafiyar Donald Trump ƙalau'

Likitan Donald Trump ya ce lafiyar kalau

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Trump ne dan takarar jam'iyyar Republican

Likitan dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump, ya ce lafiyar dan takarar kalau.

A wata wasika, likitan ya rubuta cewa "donald Trump yana cikin koshin lafiya."

Mista Trump ya saki wasikar ga jama'a, bayan duba lafiyarsa da likita Harold Bornstein ya yi.

Takardar ta bayyana mista Trump mai shekara 70 da cewa yana da tsayin da ya kai kafa 6 wato mita 1.9.

Yana kuma da nauyin 107kg.

Wannan bayani dai ya fito ne a dai-dai lokacin da ake cece-kuce kan rashin lafiyar abokiyar hamayyarsa, Hillary Clinton.

Hillary Clinton dai ta gana da 'yan jarida ranar Alhamis, a New York, a lokacin da za ta tashi zuwa New Carolina domin yin kamfe.

Wannan shi ne kamfe dinta na farko a makonnan.