Isra'ila na aikata haramci —Ban Ki-Moon

Netanyahu na son fadada kasarsa zuwa yankin Palasdinawa
Bayanan hoto,

Ban Ki-Moon zai sauka daga kujerarsa a karshen shekara

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya yi amfani da kakkausan lafazi ga firai ministan Isra'ila, Benyamin Netanyahu.

Netanyahu dai ya bayyana duk mutumin da ke adawa da shirin kasarsa na fadada yankinta zuwa yankin Palasdinawa, da mai marawa kokarin kawar da wani jinsi daga ban kasa.

Mista Ban Ki-Moon ya bayyana kalaman Netanyahu da kalamai masu matukar sosa rai.

Ya kuma ce ya kamata mista Netanyahu ya sani cewa shirin fadada girman Isra'ila haramtacce ne.

Sai dai kuma wannan na zuwa ne watanni kadan kafin Mista Ban Ki-Moon ya bar ofis, a karshen wannan shekarar.