Iraki: Burtaniya ta nemi afuwa kan kisan matashi

Ahmed Jabbar Kareem Ali, death, Basra, canal
Bayanan hoto,

Ahmed Jabbar Kareem Ali ya mutu ne a 2003 a wani tafki a Basra

Ma'aikatar tsaron Burtaniya ta nemi afuwa dangane da mutuwar wani yaro dan Iraki, mai shekara 15, wanda sojojin Burtaniyar suka tilasta wa shiga wani tafki a Basra.

Yaron mai suna Ahmed Ali na daya daga cikin 'yan Iraki da sojojin Burtaniya suka tsare bisa zargin wawason kayan da ba nasu ba, a 2003, a inda aka tilasta mu su shiga cikin tafkin lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar matashin.

Ma'aikatar tsaron ta Burtaniya ta fitar da wannan sanarwa ne da take bayar da hakuri tare da nadama bayan sukar lamirin da ake yi wa sojojin kasar a kan aikata wannan abu na inda suka kuma bar yaron ruwa ya ci shi suna gani duk da cewa sun ga bai iya ruwa ba.

Sukan yana kunshe ne a wani rahoto da aka fitar ta intanet na kwamitin da ke duba zargin ta'asar da sojojin Burtaniya suka tafka a Iraki,

Za a yi amfani da abubuwan da kwamitin binciken na tsohon alkali Sir George Newman, ya gano domin a tabbatar da cewa ba a sake aikata wani abu makamancin wannan ba.