"Yawan mutanen da suka tsere a Sudan ta Kudu ya fi miliyan"

South Sudan

Asalin hoton, AFP/Getty/Reuters

Bayanan hoto,

Shugaban kasa Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar na zargin dakarun juna da tsokanar fada ta baya-bayan nan

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da suka tsere daga Sudan ta Kudu sakamakon yakin basasar kasar ya haura miliyan daya.

Akalla mutane 185,000 daga cikin wadannan mutane kuma sun bar kasar ne bayan barkewar wani sabon fada a watan Yuli.

Galibin wadanda suka tsere a baya-bayan nan sun shiga kasar Uganda ne ko da yake dukkan makwabtan kasar sun karbi bakuncin 'yan gudun hijira tun daga lokacin da aka fara yakin.

Sai dai kuma adadin mutanen da suka bar kasar bai kai na wadanda suka guje wa muhallansu a cikin gida ba.

Su kam yawansu ya haura miliyan daya da dubu dari shida.

Hakan na nufin yakin ya tilsta wa kusan mutum guda a cikin duk mutum biyar a Sudan ta Kudu tserewa daga muhallinsu.

Yakin basasar dai ya barke ne a watan Disamba na 2013, kuma har yanzu ana ci gaba da fafatawa duk kuwa da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma bara.