Chelsea ta sha kashi a hannun Liverpool a gida

Liverpool, Henderson, Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kwallon da Henderson ya ci ita ce ta farko da ya ci wa Liverpool a wasanni 20

Chelsea ta sha kashi da ci 2-1 a hannun bakinta Liverpool a wasan mako na biyar na Premier a Stamford Bridge.

Liverpool ce ta fara jefa kwallo a ragar Chelsea ta hannun Lovren a minti na 17, sannan kuma Henderson ya kara ta biyu a minti na 36.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne Diego Costa ya ci wa Chelsea kwallonta daya tilo a karawar ta ranar Juma'a.

Da wannan nasarar yanzu Liverpool ta zama ta hudu a tebur da maki 10, yayin da Chelsea ita ma mai maki 10 take matsayi na uku da bambancin kwallo daya tsakaninsu.

Wannan shi ne rashin nasara na farko da Antonio Conte ya yi a matsayinsa na kocin Chelsea.

Wasannin mako na biyar din da za a ci gaba da yi ranar Asabar din nan su ne Manchester City da Bournemouth a Ettihad.

West Ham United za ta ziyarci West Bromwich da karawa tsakanin Leicester da Burnley.

Sai wasan Hull City da Arsenal da kuma kece raini tsakanin Everton da Middlesbrough.