Trump-'Clinton idan kin isa ki ajiye makamanki'

Donald Trump, Hillary Clinton, guns
Bayanan hoto,

Trump ya ce zai so ya ga dogarawan Clinton sun zubar da bundugogin kare ta

Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump, ya zolayi abokiyar hamayyarsa ta Democrat, Hillary Clinton da ta zubar da bundigoginta na kare kai.

Da yake jawabi a wurin yakin neman zabensa a Miami, Mista Trump, ya ce, Madam Clinton na neman watsa tanadin kundin tsarin mulkin Amurka ne da ya ba wa 'yan kasar damar mallakar makami.

Donald Trump ya hau dandamalin yakin neman zabensa a Miami yana me sukar matsayin Hillary Clinton a kan maganar mallakar bindiga.

Mr Trump ya yi kururuwa yana daga murya ga mahalatta gangamin yakin neman zaben nasa, yana ce musu, ''ai na dauka masu kare lafiyar 'yar takarar ta Democrat nan da nan da maganarta za su ajiye makamansu, su tsaya haka sasakai.

Ya gaya wa magoya bayan nasa cewa, ''to da sai mu ga abin da zai faru da ita''

An soke shi a watan da ya wuce a kan irin wannan kalami, wanda a wancan lokacin ya ce idan aka zabi Hillary Clinton shugabar Amurka, kuma ta nada alkalan kotun koli, to ba abin da wani zai iya yi a kan wannan magana.

Amma kuma nan da nan sai ya kara da cewa, kila idan aka yi la'akari da dokar da ta ba wa Amurkawa damar mallakar makami, akwai abin da za a iya yi akai.

A kan kalaman nasa wasu 'yan jamiyyar ta Democrat sun ayyana hakan a matsayin wata barazana ta yunkurin kisan 'yar takarar tasu, abin da jami'an yakin neman zabensa suka yi watsi da shi da cewa barkwanci ne kawai.

A martanin jagoran yakin neman zaben 'yar takarar ta Democrat Robby Cook, ya ce, ''ai daman Donald Trump, dan takarar jam'iyyar Republican yana da dabi'a ta haddasa fitina.

Kuma bai dace a ce mutumin da ke neman zama shugaban Amurka ba yana irin wadannan kalamai, to amma daman sun fahimci cewa wannan abu ne da ya zama jiki ga Mista Trump.

Ya kara da cewa mutum ne da bai dace da shugabancin Amurka ba, kuma lokaci ya yi da shugabannin jam'iyyar Republican za su fito fili su yi Allah-wadai da wannan dabi'a ta dantakarar nasu.