Zargin cin hanci: Cikas ga zaman lafiya a Sudan ta Kudu

Outh Sudan President

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaba Salva Kiir

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta ce rahoton baya-bayan nan da wata kungiya a Amurka ta fitar, inda ta zargi wasu manyan jami'an kasar da cin hanci da rashawa, zai kawo tarnaki ga yunkurin tabbatar da zaman lafiya.

Kakakin shugaba Salva Kiir, wanda aka ambato sunanshi a cikin rahoton ya kalubalanci rahoton, yana mai cewa, babu wani shugaba daga kasashen Turai da zai yarda a yi mushi irin wannan zargi ba tare da hujjoji ba.

A wasu lokuta, bangaren shugaba Salva Kiir ya na zargin kasashen yammaci da kulle-kullen sauya gwamnati a Sudan ta Kudun.

Rahoton wanda kungiyar mai suna Sentry, da wani jarimin fina-finan Hollywood, George Clooney suka fitar, ya ce shugabannin Sudan ta Kudun suna cin kazamar riba, yayin da jama'ar kasar ke shan bakar wahala saboda yakin basasa a kasar.

Mutane da dama sun tsere

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da suka tsere daga Sudan ta Kudu sakamakon yakin basasar kasar ya haura miliyan daya.

Akalla mutane 185,000 daga cikin wadannan mutane kuma sun bar kasar ne bayan barkewar wani sabon fada a watan Yuli.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Rikicin ya raba mutane da dama da muhallansu

Galibin wadanda suka tsere a baya-bayan nan sun shiga kasar Uganda ne ko da yake dukkan makwabtan kasar sun karbi bakuncin 'yan gudun hijira tun daga lokacin da aka fara yakin.

Sai dai kuma adadin mutanen da suka bar kasar bai kai na wadanda suka guje wa muhallansu a cikin gida ba.

Su kam yawansu ya haura miliyan daya da dubu dari shida.

Hakan na nufin yakin ya tilsta wa kusan mutum guda a cikin duk mutum biyar a Sudan ta Kudu tserewa daga muhallinsu.

Yakin basasar dai ya barke ne a watan Disamba na 2013, kuma har yanzu ana ci gaba da fafatawa duk kuwa da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma bara.