Jami'ai sun taimaka ma yaro mutuwa a Belgium

Belgium euthanasia

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Belgium ce kadai a duniya da ke ba yara damar zabin mutuwa

A Belgium, a karon farko tun bayan bullo da dokar amincewa yara masu fama ciwon da ba a warkewa su nemi a dauki rayuwarsu, jami'ai a kasar sun taimaka wa wani yaro ko yarinya mutuwa.

Hukumomi a kasar sun tabbatar da hakan, amma ba su yi karin bayani ba game da shekaru da jinsin wanda aka taimakama wa daukar rayuwarshi.

Belgium ce ka dai a duniya da ta amince yara, 'yan kowacce shekara su zabi su mutu.

Duk wata bukata ta neman mutuwa, dole ne ta kasance yaran ne suka gabatar da ita, sannan dole sai kwararrun likitoci da masana halayyar dan adam sun yi nazari akanta, tare kuma da amincewar iyayensu.

Masu aiko da rahotanni sun ce dokar ta haifar da rabuwar kai a Belgium, inda wasu ke kalubalantar bai wa yara damar yanke irin wannan hukunci.