Yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria na neman lalacewa

Syria

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Rasha ta zargi Amurka da jan kafa

Jami'an Rasha sun yi gargadin cewa lamari a kasar Syria na kara tabarbarewa, yayin da 'yan tawaye suka kai hare-hare fiye da hamsin akan dakarun gwamnati a cikin sa'o'i ashirin da hudu da suka wuce.

Wani Janar na sojin Rasha ya zargi Amurka da gaza cika nata bangaren na yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria.

Janar Viktor Poznikhir ya yi gargadin cewa Amurka ce za dorawa laifi idan har yarjejeniyar ta sukurkuce.

A ranar Juma'a, Amurka ta zargi Rasha da gazawa wajen matsawa gwamnatin shugaba Bashar Al-Assad na ta bari ayarin motocin kayan agaji su samu shiga garuruwa da biranen Syria da aka yi wa kawanya.