Mutanen da suka mutu a harin Pakistan sun kai 30

Pakistan
Bayanan hoto,

Akasarin wadanda suka mutu a harin yara ne

An sanyar dokar hana fita a wani yanki na arewa maso gabashin Pakistan, inda wani dan kunar bakin wake ya halaka gwamman mutane ranar Juma'a.

'Yan sanda na ci gaba da farautar 'yan bindigan da ake gani suna da hannu a harin a Masallaci.

Adadin mutanen da aka tabbatar sun mutu kawo yanzu, ya kai talatin.

An kai harin ne lokacin da ake sallar Juma'a, kuma rahotanni daga kauyen da ke yankin kabilar Mohmand, sun ce akasarin wadanda suka mutun yara ne.

Wani bangare na kungiyar Taliban, Jama'atul-Ahrar, ya ce shi ne ya kai harin, kuma ta yi fakon 'yan banga ne masu yaki da Taliban.