Dokar halatta kashe kai ta fara aiki a Belgium

mmmercy killing, euthanasia, belgium

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dokar ba wa mai cutar ajali damar kawo karshen rayuwarsa ta raba kan mutanen Belgium

Likitoci a Belgium sun taimaki wani matashi mai kimanin shekara 17 maras lafiya ya kashe kansa, bayan da cutar da yake fama da ita ta tsananta.

Wannan dai shi ne karon farko da likitoci suka fara ba wa marassa lafiyar da suka gaji da duniya, maganin mutuwa, tun bayan da aka kirkiro dokar da ta amince da yin hakan.

Belgium ce kasar da a duniya ta ba wa yara 'yancin kashe kansu sakamakon matsananciyar rashin lafiya musamman idan har sun kai shekarun da za su iya yanke wa kansu hukunci.

A dokar dole ne, yaron ne da kansa zai zabi ya mutu, sannan wasu likitoci da wani kwararren masanin halayyar dan adam me zaman kansa da kuma iyayen yaron, za su yi nazarin zabin yaron na mutuwar.

Amma kuma wannan abu ne da ba kasafai ake samu ba, da zai kai ga yin wannan mutuwa ko kisa da ake kira kisa na tausayi.

Wannan dai batu ne da ya rarraba kan jama'a a kasar ta Belgium, inda shugabannin coci da wasu likitoci suke shakkun dacewar dokar da za a ce ta ba wa yara ikon su yanke irin wannan shawara mai wuya.

Daya daga cikin wadanda suka sa a yi dokar Sanata Jean-Jacques De Gucht, ya ce dole ne a bari yaran da suke yanayi na mutuwa su zabi abin da suke so.

Domin a cewarsa ba za ka iya kwatanta babban mutumin da bai gamu da wata cuta ba, da matashin da yake fuskantar mutuwa.

Sanatan ya ce, dokar tana kuma taimaka wa likitoci, domin a irin wannan yanayi, wani lokaci ba a san mawuyacin halin da likitoci ke ciki ba, akan maras lafiyar da ke fama da cutar da ba ta tashi ba.

Ya ce a don haka dole ne a ba su tabbaci da kuma kyakkyawan yanayi na kariya ta doka da za su yi aikinsu.

A Burtaniya an haramta wannan dama ko kisa da maras lafiya da ke fama da cutar ajali zai zabi a kawo karshen rayuwarsa ta hanyar ba shi wani magani ko allura.

Sai dai duk wanda yake fama da rashin lafiyar da aka tabbatar ba zai warke ba, ya ki yarda a yi masa magani ko kuma ya zauna a gida a rika kula da shi har wa'adinsa ya cika.