Wani abu ya fashe a New York

Ana dai yawan samun fashewar abubuwa a Amurka
Bayanan hoto,

Mutane 29 ne suka jikkata sakamakon tarwatsewar abin

Mutane 29 ne suka samu rauni sakamakon fashewar wani abu a gundumar Chelsea da ke Manhattan na birnin New York.

'Yan sanda sun ce suna zaton cewa abun fashewar ne ya yi awon gaba da tagar wani gini da kuma wata mota.

Hotuna a kafafe sada zumunta sun nuna yadda wani kwandon shara ya tarwatse sakamakon fashewar.

Hakan dai ya faru ne sa'o'i kadan bayan wani bam ya tashi a kwandon shara, a New Jersey.

Bam din ya tashi ne a kusa da wani wuri za a gudanar da gasar tseren sojoji.