Al-Shabab ta halaka wani janar din soji a Somalia

Somalia

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mayakan Al-Shabab

Wani harin bom a Mogadishu, babban birnin Somalia ya halaka wani Janar na sojin kasar tare da wasu masu tsaron lafiyarsa.

Wasu rahotanni sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya danna da wata mota mai dauke da bama-bamai cikin ayarin motocin Janar Mohamed Jimale Goobaale.

Harin ya auku ne a kusa da shedkwatar tsaro ta kasar.

Mayakan kungiyar Al-Shabab sun ce su ne suka kaddamar da harin, inda suka zargi Janar din da yin kulle-kullen ganin bayansu.