An kashe mutane 20 a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka

UN Minusca peacekeepers

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD a Jamhoriyar Tsakiyar Afrika a 2014

Rundunar wanzar da zaman lafita ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane ashirin ne aka kashe a fadan daya kaure tsakanin kungiyoyin 'yan tawaye da basa ga maciji da juna a Jamhoriyar Tsakiyar Afirka.

Dakarun Majalisar Dinkin Duniyan sun ce sun shiga tsakani don hana ci gaba da tashin hankali a garin Kaga Bandoro dake arewaci, kusa da inda aka yi kashe kashen.

Wani mai magana da yawun fadar shugaban kasar ya ce adadin mutanen da aka kashen ya kai ashirin da shida.

Ya yi zargin cewa 'yan tawaye na kungiyar Saleka sun rika bi gida-gida suna kashe mutanen.

Jamhoriyar tsakiyar Afirkan dai ta yi ta fama da tashe-tashen hankali na addini tun a watan Maris na 2013, lokacin da 'yan tawayen Saleka suka karbe mulkin kasar na wani gajeren lokaci daga hannun shugaba Francois Bozize.

Daga baya, aka hambarar da gwamnatin da Salekan ta kafa, abin da ya janyo tashin hankali tsakanin 'yan tawayen kungiyar dana anti-Balaka.

Dubban mutane ne aka kashe, yayin da wasu dubban kuma suka rasa gidajensu tun a 2013.

Dakaru dubu goma sha daya na Majalisar Dinkin Duniya ne aka girke a kasar domin aikin wanzar da zaman lafiya.