An sako mukarraban Hama Amadou a Niger

Soumana Sanda

Asalin hoton, nigerdiaspora.net

Bayanan hoto,

Soumana Sanda na cikin mukarraban Hama Amadou da aka sako bayan wat 10 da kama su

Rahotanni daga Nijar sun ce an sako wadansu 'yan adawa bakwai, ciki har da wani tsohon ministan lafiya, wata 10 bayan daure su a gidan kaso.

Gaba dayan mutanen bakwai dai na-hannun-daman tsohon Kakakin Majalisar Dokoki Hamma Amadou ne wadanda aka zarga da shirya tarurruka da daukar makamai ba bisa ka'ida ba.

Kamfanin dillancin labarai na Faransa, AFP, ya ambato wani jami'ar a jam'iyyar MODEN Lumana, Seini Moukaila, yana cewa "An sako Soumana Sanda da 'yan uwansa shida da aka tsare bayan sun yi zaman kaso na wata 10".

Sai dai kuma kafofin yada labarai na Nijar sun ce a wata tattaunawa da ya yi da 'yan jarida bayan fitowarsa, Soumana Sanda ya ce shi da wadansu mutanen biyar aka sako.

Ranar 14 ga watan Nuwamba na bara ne dai aka kama mutanen bayan da jami'an tsaro sun yi taho-mu-gama da 'yan jam'iyyar wadanda suka taru don tarbar Hama Amadou.

Shi ma dai shugaban jam'iyyar tasu a ranar aka kama shi bayan dawowarsa daga gudun hijira a Faransa.