An kashe mutum 17 a zanga-zangar adawa da gwamnatin DR Congo

Asalin hoton, Reuters
Daruruwan mutane ne suka halarci zanga-zangar
Akalla mutane 17 ne suka mutu a zanga-zangar da aka shirya domin tilasta wa Shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo ya yi murabus.
A cewar ministan cikin gida, Evariste Boshab, uku daga cikin wadanda suka rasa rayukansu 'yan sanda ne, kuma an kona daya ne da ransa.
Masu zanga-zangar sun kafa shingaye, sannan suka farfasa motoci a daya daga cikin manyan hanyoyin Kinshasa, babban birnin kasar.
'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar.
Wani da ya shaida lamarin ya ce 'yan sandan sun budewa gangamin mutanen wuta.
An ga gawarwakin mutanen da aka kashe a kan tituna bayan kammala zanga-zangar.

Asalin hoton, Getty Images
Mista Kabila ya hau mulki a shekarar 2001 bayan an kashe mahaifinsa Laurent Kabila
A ranar Litinin ne aka tsara hukumar zaben kasar za ta sanar da ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa a watan Nuwamba.
Sai dai hukumar ta ce ba zai yiwu a gudanar da shi ba.
'Yan adawa sun ce Mista Kabila na kokarin dakile zaben ne domin ya ci gaba da kasancewa a kan mulki, bayan kammala wa'adinsa a watan Disamba.

Asalin hoton, AP
Masu zangza-zangar sun kona motoci

Asalin hoton, Reuters
An tura 'yan sandan kwantar da tarzoma a kan titunan birnin Kinshasa