Wani abu da ake zargi bam ne ya fashe a filin jiragen kasa a New Jersey

Butumbutumi ya yi kokarin cire na'urar da ake zargi bam ne

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Wata na'ura ta fashe a wani filin jirgin kasa a New Jersey

Wani abu da ake zargin bam ne da aka gani a kusa da tashar jiragen kasa ta garin New Jersey a Amurka, ya fashe a lokacin da jami'an kwance bam ke kokarin cire shi da butum-butumi.

Magajin garin ya ce na'urar da ta fashe, daya ce daga cikin na'urori guda biyar da aka gani a cikin wata jaka da aka saka cikin wani kwandon shara a kusa da filin jirgin kasa na Elizabeth.

Ya kara da cewa babu wanda ya jikkata a lamarin.

Wannan na faruwa ne bayan hare-hare uku da aka kai a karshen makon da ya gabata inda aka samu tashin bama-bamai a New York da New Jersey da kuma hari da wukake a garin Minnesota.

Bam din na New York ya tashi ne a yankin Chelsea da ke birnin inda ya jikkata mutane 29.