Nigeria: Kungiyar musulumai ta gargadi makarantu kan saka hijabi

An gargadi makarantu kan saka hijabi
Bayanan hoto,

Kungiyar musulumai a Nigeria ta gargadi makaratu kan saka hijabi

Wata kungiyar Musulmai a Nigeria ta gargadi makaratun gwamnati da ke jihar Lagos da kar su hana mata daura dankwali ko kuma saka hijabi.

A cewar jaridar Vanguard, gargadin ya zo ne a daidai lokacin da dalibai za su koma makaratunsu a karo na farko domin fara karatun sabuwar shekara na makaranta.

A watan Yuli ne dai wata kotun daukaka kara, ta dage takunkumin da aka sakawa dalibai mata na hana su saka hijabi.

Jaridar Vanguard ta ambato Saheed Ashafa, babban mai wakiltar kungiyar Musulmai a Najeriya yana cewa makaratu za su saba dokar kotu idan har suka kama dalibai ko suka hukuntasu saboda saka hijabi.

Shugaban kungiyar kare hakkin Musulmai ta Najeriya Farfesa Ishak Akintola ya shaidawa BBC cewar kungiyar ta na san ran gwamnatin Lagos za ta sanar da makarantu hukuncin da kotu ta yanke na dage takunkumi saka hijabi a makarantun gwamnati a Jihar.

Ya kuma kara da cewar kungiyar, wacce yake jagoranta, tana saka ido domin tabbatar cewar makarantu ba su saba hukuncin kotun ba.