New York: 'Yan sanda sun tsare Ahmad Khan bayan ya harbi wani jami'i

Bam din New York ya kashe mutane da dama

Asalin hoton, NYPD

Bayanan hoto,

Ahmad Khan Rahami ake zargi da saka bam a New York

'Yan Sanda suna tsare da mutumin da ake zargi da kai harin bam a New York bayan da ya harbi wani dan sanda a garin Linden da ke New Jersey.

Hotunan bidiyo da aka wallafa a intanet ya nuna Ahmad a kan gadon da ake daukar marasa lafiya.

Linden dai na kusa da birnin Elizabeth inda aka samu wasu na'urorin a yammacin rananar Lahadi.

Lamarin dai ya afku ne bayan 'yan sanda sun gano Ahmad a matsayin wanda ake zargi kuma ake so ayi wa tambayoyi a kan bam din da aka saka a yankin Chelsea da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 29.

An gano Ahmad Khan Rahami mai shekaru 28, a matsayin mutumin da ake zargi kuma haifaffen kasar Afghanistan ne wanda ya samu shaidar zama dan kasar Amurka.

'Yan sanda a New York sun wallafa hoton shi.

A safiyar ranar Litinin ne dai wata jaka mai dauke da wasu na'urori guda biyar ta fashe a garin Elizabeth da ke New Jersey, a lokacin da wani butum-butumi ya ke kokarin fitar da ita.

Masu bincike dai sun yi gargadin cewar mutumin da ake zargin ya kai harin, wanda ya taba zama a Elizabeth "yana dauke da makamai kuma yana da hadari".

Magajin Garin New York, Bill de Blasio ya fada wa CNN cewar "duk wanda ya ga mutumin ko kuma ya san wani abu game da shi ya kamata a sanar da hukuma ba tare da ba ta lokaci ba".