Amurka: An tuhumi Ahmad Khan da yunkurin kashe 'yan sanda

Ana tuhumar Ahmad Khan da laifuka biyar

Asalin hoton, Nicolaus Czarnecki

Bayanan hoto,

An kama Ahmad Khan bayan musayar wuta

An tuhumi mutumin da ake zargi da kai harin bom a New York da New Jersey, wato Ahmed Khan Rahami da aikata laifuka biyar da suka shafi yunkurin kashe yan sanda.

An dai cafke Ahmed Khan Rahami ne bayan musanyar wuta da `yan sanda, inda aka jikkata shi, kuma a halin da ake ciki ana masa jinya a wani asibiti.

Watakila a tuhume shi da aikata wasu laifukan da suka shafi harin bom a nan gaba.

Magajin garin New York, Bill de Blasio ya ce babu tantama hare-haren da ake zargin Ahmed Khan Rahami da kaiwa, na ta`addanci ne.

Shugaba Barak Obama ya ce kokarin da jami`an tsaro suka yi wajen cafke mutumin da ake zargin abin a yaba ne, kana ya bukaci al`umar Amurka da su kwantar da hankalinsu.