Kano: Har yanzu ba a tallafawa 'yan kasuwar Sabon Gari ba

Yan kasuwan Sabon gari na neman tallafi daga wajen gwamnati
Bayanan hoto,

'Yan kasuwar sabon gari sun tafka asarar miliyoyi a gobarar da ta afku a watan Maris

'Yan kasuwar Sabon Gari a birnin Kano sun koka a kan rashin samun tallafi daga wajen gwamnati, wata shida bayan mummunar gobarar da ta kona rumfa 4,000 a kasuwar.

Gobarar wacce ta afku a watan Maris, ta haddasa gagarumar asara a babbar kasuwar, inda 'yan kasuwar suka sayar da kadarori wasu kuma suka yi rance domin gyara rumfunansu da suka kone.

Sai dai da dama daga cikin shagunan, wadanda aka gyara bayan afkuwar gobarar, ba su da kaya sosai saboda rashin jari.

Mallam Nasiru Mu'azu, daya ne daga cikin mutane da dama da suka yi asarar shagunansu a gobarar kuma ya ce ya saki shagonsa wanda wuta ta cinye, inda ya koma kasa kaya a tebur.

Ya kara da cewa ya yi asarar kudi kusan miliyan uku.

Amma gwamnatin jihar Kano ta ce tana sane da halin da 'yan kasuwar suke ciki.

Kwamishinan yada labarai na jihar Muhammad Garba, ya ce "an gama tsare-tsaren da za a yi domin kaddamar da asusun neman taimako wanda zai bai wa gwamnatin damar bayar da tallafin da 'yan kasuwar ke bukata".

Sai dai bai bayyana takamaiman lokacin da za ta bai wa 'yan kasuwar tallafin ba.

A daidai lokacin da 'yan kasuwar Sabon Gari ke kokarin farfadowa daga gobarar da faru a watan Maris, matsalar tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta da karancin ciniki na cigaba da kawo musu tsaiko.