Zanga-zanga a DR Congo: An kona ofisoshin 'yan adawa

An gano gawarwakin mutanen da aka kona a ofishin babbar jam'iyyar adawa
An kona ofisoshin jam'iyyun adawa uku a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, sannan aka cinnawa wasu mutum biyu wuta a Kinshasa, babban birnin kasar.
Harin ya zo ne kwana guda bayan mummunar tarzomar da ta barke tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar adawa da Shugaba Joseph Kabila.
Suna bukatar da ya bar mulki ne a watan Disamba lokacin da wa'adinsa zai kare.
Ofishin babbar jam'iyyar adawa ta UPDS na daga cikin wadanda aka kona a Kinshasa.
Jam'iyyar ta gargadi Mista Kabila da cewa jinkirta zaben kasar "cin amanar kasa ne".
A watan Nuwamba ne aka tsara gudanar da zabukan, sai dai 'yan adawa na zargin shugaban na son dage zaben ne domin ya ci gaba da zama a kan mulki.
Sai dai har yanzu Mista Kabila bai ce komai game da shirin na sa ba.
An kuma kai hari ofishin kana nan jam'iyyun adawa
Kundin tsarin mulkin kasar ya hana shugaban, wanda ya hau mulki a 2001 bayan kisan mahaifinsa Laurent Kabila, sake yin takara.
Ba a taba mika mulki cikin lumana a kasar ba tun bayan da ta samu 'yan cin kai shekaru 55 da suka gabata.
Hukumomi sun ce akalla mutane 17 ne aka kashe a tarzomar ta ranar Litinin, ciki har da 'yan sanda uku wadanda aka kona su da ransu.
"Yan adawa sun ce mutane 50 ne aka kashe.
Wakilin BBC a Kinshasa ya ce babu tabbas kan ko su wanene suka kai harin na baya-bayan nan.