Zaben Amurka: Hillary Clinton zan zaba - George HW Bush

Tsohon shugaban kasar Amurka shugaba George HW Bush da matarsa Former President George HW Bush and his wife Barbara Bush watch the 2015 NCAA Men's Basketball Tournament in Houston, Texas - March 29, 2015

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Har yanzu Mista Bush da matarsa Barbara basu goyi bayan Donald Trump ba

Tsohon shugaban Amurka a karkashin jam'iyyar Republican George HW Bush ya ce 'yar takarar jam'iyyar Democrat Hillary Clinton zai zaba a zaben da za a yi a watan Nuwamba.

A cewar shafin labarai na Amurka US news website Politico, Mista Bush ya yi alkawarin ne a lokacin da ya ke ganawa da Kathleen Kennedy Townsend, 'yar uwar tsohon Shugaban Amurka John F Kennedy.

Ofishin tsohon shugaban bai ce komai ba game da rahoton ba.

Mai magana da yawunsa ya ce yana cigaba da bincike kan labarin, lokacin da aka tuntube shi kan lamarin.

Mista Bush, wanda ya shugabanci Amurka daga shekarun 1989 zuwa 1993, bai fito fili ya goyi bayan dan takarar jam'iyyarsu ta Republican, Donald Trump ba.

Haka kuma dansa, Jeb Bush, wanda ya sha kayi a zaben fitar da gwani a hannun Mista Trump, da ma sauran wadanda suka yi takara da shi Ted Cruz da John Kasich.