Angelina Jolie 'za ta rabu da mijinta Brad Pitt'

Brad Pitt and Angelina Jolie

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mutanen biyu sun kasance tare tun shekarar 2004

Launyan fitacciyar jarumar fim din nan Angelina Jolie ya ce ta nemi a raba auranta da Brad Pitt.

Robert Offer ya ce jarumar ta shigar da bukatar hakan ne a ranar Litinin, yana mai cewa ta dauki matakin ne domin "tabbatar da lafiyar zuri'ar ta su".

Ya kara da cewa Mis Jolie ba za ta ce komai ba, sannan ya bukaci jama'a da su bai wa iyalan na ta sarari domin su fuskanci halin da suke ciki.

Jolie da Pitt sun kasance tare tun shekarar 2004 amma sai a watan Agustan 2014 ne suka yi aure.

Suna da 'ya'ya shida - Maddox da Pax, da Zahara da Shiloh da kuma yan biyu Knox da Vivienne.

Brangelina: Yadda suka hadu

Asalin hoton, PA

Jolie da Pitt - wadanda magoya bayansu ke wa lakabi da "Brangelina" - na daya daga cikin ma'auratan da suka fi yin fice a fagen fina-finan Hollywood na Amurka.

Sun fara soyayya ne bayan da suka hadu a wani fim a 2005.

Fim dinsu na baya-bayan nan shi ne By The Sea - wanda na soyayya ne wanda Jolie ta shirya.