Bukola Saraki: 'Yan Nigeria na fama da yunwa

Bukola Saraki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mista Saraki ya ce batun wanda ya jawo matsalar da aka shiga ba shi ne a gaban 'yan kasar ba

Shugaban Majalisar Dattawan Nigeria Bukola Saraki ya ce 'yan kasar da dama na fama da yunwa, kuma wajibi ne a fito da hanyoyin magance matsalar tattalin arzikin da ake fama da ake fuskanta.

Mista Saraki na jawabi bayan dawowar majalisar daga hutun watanni biyu, ya ce za su shafe watanni masu zuwa domin mayar da hankali kan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Ya ce wajibi ne "mu lalubo hanyoyin da za su saukaka wa jama'a halin kuncin da suke ciki ba tare da la'akari da banbancin siyasa ba.

Ya yi kira da a gudanar da muhawara ta gaskiya kan batun tattalin arzikin Najeriyar.

"Mutane ba su damu da wanda ya jefa kasar cikin wannan hali ba, illa dai kawai suna neman mafita ne," in ji Sanata Saraki.

"A zahiri take cewa a lokacin da mutane ke cikin yunwa, to babu abin da suke bukata sai jagoranci nagari, wanda zai nuna damuwa da halin da suka samu kansu a ciki".

A don haka ya ce wajibi ne shugabanni su mayar da hankali wurin shawo kan matsalar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mista Saraki (daga hagu) ya nemi bangaren zartaswa da su fito hanyoyin shawo kan matsalar

Ya nemi bangaren zartaswa da su dauki matakan gaggawa domin farfado da harkokin kasuwanci da zuba jari.

Ya kuma nemi 'yan majaliasar da su baiwa bangaren zartaswa hadin kai wurin fito da dokokin da za su taimaka wurin ciyar da tattalin arzikin kasar gaba.

Sai dai ya amince cewa al'amura ba za su sauya cikin gaggawa ba, inda ya yi kira ga jama'a da su kara hakuri, yana mai cewa kasar za ta samu mafita nan gaba kadan.

A ranar Laraba ne majalisar za ta fara muhawara gadan-gadan kan batun tattalin arzikin Najeriyar, wanda a hukumance aka tabbatar cewa ya samu tawaya.