An kori ministan kudin Iraki saboda cin hanci

Ministan Kudin kasar Hoshyar Zebari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hoshyar Zebari gogaggen dan siyasa ne

Majalisar dokokin Iraki ta kada kuri'ar korar Ministan Kudin kasar, Hoshyar Zebari, daga mukaminsa, bisa zarge-zargen cin hanci.

A makon jiya ma an cire ministan tsaron kasar daga mukaminsa, shi ma bisa zarge-zargen cin hancin.

Wannan na nufin kasar ba ta da muhimman ministoci guda biyu ke nan a lokacin da take fuskantar kalubalen tattalin arziki da kuma tsaro.

Mista Zebari sanannen dan siyasa ne a Irakin, wanda a baya ya rike mukamin ministan harkokin waje na tsawon shekaru da dama.

A baya-bayan nan ne dai ya jagoranci wata tawaga mai karfi zuwa wata tattaunawa da Asusun Ba da Lamuni na Duniya, IMF, don kokarin cim ma yarjejeniya a kan bai wa kasar rance.

Rikicin siyasa ya dade yana addabar kasar ta Iraki, wacce ke kuma fama da rikicin addini da kuma na kungiyar IS.