Wata 'baƙuwar' cuta ta kashe mutum 21 a Nijar

Hukumomi sun ce za su dauki mataki

Asalin hoton, ISSOUF SANOGO

Bayanan hoto,

Dabbobi ne ke haddasa cutar

Hukumomin kula da lafiya a Jamhuriyar Nijar sun ce wata baƙuwar cuta da ta bulla a yankin Tahoa ta kashe mutum akalla 21.

Cutar, wadda ake dauka daga jikin dabbobi, ta bulla ne a 'yan kwanakin da suka gabata.

Wasu jami'an ma'aikatar lafiya ta kasar sun shaida wa BBC cewa ana iya daukar cutar ta hanyar shan nonon dabbar da ke dauke da ita.

Sun kara da cewa suna daukar matakai domin shawo kan wannan cuta da ke saurin yaduwa.