Amurka ta dora wa Rasha alhakin harin da aka kai kan motocin agaji

Amurka ta dora wa Rasha alhakin harin

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

An kai hari kan motar ne a lokacin da ta ke sauke kayan agaji

Amurka ta ce ta dora wa kasar Rasha alhakin mummunar harin da aka kai ranar Litinin kan jerin gwanon motocin agaji a kusa da garin Aleppo.

Fadar shugaban kasar Amurka ta kira harin "wani babban bala'i da ya shafi masu bayar da agaji".

Jami'ai a Amurka sun shaida wa BBC cewar jiragen sama na yaki na kasar Rasha ne suka kai harin.

Sai dai Rasha ta musanta zargin inda ta dage kan cewar jiragen saman yaki na kasarta da na Syria ba su da hannu a harin.

Ta kuma kara da cewar lamarin ya afku ne sakamakon wuta a kasa ba harin sama ba.

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaron kasar Rashan ta fitar ta ce "Lalacewar da wajen motar ta yi bai yi kama da harin bam ne daga sama ba".