Hukumomi a kasar Zimbabwe sun gargadi 'yan kasar a kan wulakanta Tuta

za a saka masu wulakanta tuta a kurukuku

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan kasar Zimbabwe na neman sauyi a gwamnatin kasar

Hukumomi a kasar Zimbabwe sun gargadi 'yan kasar cewa suna fuskantar hadarin shiga gidan yari idan suka wulakanta tutar kasar yayin wata zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Wadanda suka wulakanta tutar za su biya tarar $200 ko kuma su yi wata shida a gidan yari a cewar ma'aikatar shari'a.

A wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar ta ce ba a yarda a sayar da tutar kasar ba tare da izini daga ma'aikatar shari'ar ba.

Masu zanga-zangar dai na amfani da tutar a matsayin wata alama ta kira ga gwamanti na neman kawo sauyi inda suke amfani da maudu'in #ThisFlag a Twitter.

A watan Afrilu ne dai wani fasto ya saka bidiyonshi da tutar a nade a wuyanshi a shafinsa na Facebook.

A bidyon, faston ya yi kira ga 'yan Zimbabwe, wadanda suka gaji da yadda ake gudanar da harkokin kasar, da su tashi tsaye domin ganin an kawo sauyi.