Har yanzu Malam Fatori 'na hannun Boko Haram'

Tutar Boko Haram a garin Damasak, Nigeria (18 March 2015)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Boko Haram na dora tutarta a garuruwan da ta kwace

Wata majiyar soji ta shaida wa BBC cewa har yanzu garin Malam Fatori na jihar Borno na hannun kungiyar Boko Haram, sabanin ikirarin da rundunar sojin Nigeria ta yi cewa ta kwace shi.

Wani jami'in soji da ya nemi a boye sunansa, ya ce babu gaskiya a ikirarin da rundunar ta yi cewa ta fatattaki mayakan Boko Haram daga garin.

Ya kara da cewa sojojin Najeriya da suka yi yunkurin kwace garin a ranar Talata sun janye, kuma an kashe wasu daga cikinsu, yayin da har yanzu ba a ga wasunsu ba.

A ranar Talata ne kakakin rundunar sojin Kanar Sani Usman, ya shaida wa BBC cewa sun kwace garin, wanda ke kan iyakar Najeriya da Nijar, daga hannun Boko Haram.

Sai dai rahotanni daga yankin tafkin Chadi na cewa ana cigaba da gumurzu a tsakanin rundunar sojin gamayya ta kasashen dake makwabtaka da tafkin da masu tayar da kayar bayan.

Shi ma dai Kanar Usman ya tabbatar da cewa sun fuskanci mummunar turjiya, kuma ana cigaba da gwabza kazamin fada.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An tura sojoji da dama zuwa yankin Arewa maso Gabashin Najeriya

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani a kan irin halin da ake ciki a garin na Malam fatori saboda rashin hanyoyin sadarwa.

Kungiyar Boko Haram dai ba ta ce komai game da wannan fadan ba kawo yanzu.

Amma kungiyar IS wadda Boko Haram ke wa mubayi'a ta wallafa a shafinta na yanar gizo cewa an halaka akalla sojoji arba'in bayan sun kai wa wani ayarin motocin sojin hari, sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari.

A baya dai mayakan Boko haram sun kwace tare da yin iko da wurare da dama a Arewa maso Gabashin Najeriya dama wasu wuraren a kasahen da ke makwabtaka da tafkin Chadi.

Sai dai rundunar Sojin Najeriya da ta makwabtanta sun fatattakesu tare da kwace yawancin wuraren, amma bisa ga dukkan alamu har yanzu suna rike da iko da wasu wuraren sabanin rahotannin da sojojin ke bayarwa.