Daga nahiyar 'Afirka dan adam ya fara rayuwa'

Afirka ce asalin kowa a duniya

Asalin hoton, Scince Photo Library

Bayanan hoto,

Mutanen farko mafarauta ne da ke yawo a duniya domin farauta

Masana kimiyya sun samo wata shaida da ke jaddada hasashen da ake yi cewa asalin bil`adama baki daya sun fara wanzuwa ne a nahiyar Afirka.

Bincike daban-daban har sau biyu wadanda aka wallafa a cikin mujallar "Nature" sun nuna cewa za a iya bibiyar salsalar daruruwan mutane a duniya zuwa ga wata al`umma tilo a nahiyar Afirka, kuma sun yi hijira ne daga Afirka zuwa wasu bangarorin duniya a tsakanin shekaru 40,000 zuwa 80,000 da suka shude.

Masu binciken sun bi diddigin kwayoyoin halittar wasu mutane ne a fadin duniya, sannan suka yanke hukunci cewa tushensu daya ne da suka yi kaura daga Afirka.

To sai dai binciken ya kuma gano wasu mutanen dake zaune a Papua New Guinea a yankin Pacific da kwayoyin halittarsu suka nuna cewa sun yi kaura daga Afirka wajen shekaru 100,000 zuwa shekaru 120,000, kuma tushensu daban yake.

Binciken ya gano cewa, bayan dan adam ya fara rayuwa a Afirka shekaru 200,000 da suka gabata, mutane sun fara yin kaura, inda suka bi ta Masar zuwa yankin kasashen Larabawa, shekaru 60,000 da suka wuce.

Sannan akwai wasu mutanen da suka taba rayuwa a duniya da ba lallai Afirka ce tushen su ba.

To sai dai masu binciken sun hakikance cewa ko da asalin wadannan mutane ba daga Afirka ya ke ba, to babu sauran irinsu da ke rayuwa, tuni sun jima da karewa gaba dayansu.