'Yan sanda sun nemi tarwatsa zanga-zangar 'yan Shi'a a Abuja

'Yan Shi'a a Nigeria

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Ana tsare da Sheikh Ibraheem Zakzaky tun watan Disamba

Kungiyar 'yan Uwa Musulmi wacce aka fi sani da 'yan Shi'a a Najeriya sun gudanar da zanga-zangar lumana a Abuja, babban birnin kasar domin kira ga hukumomi su saki shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

'Yan kungiyar sun koka kan yadda jami'an tsaron kasar ke ci gaba da tsare shugaban nasu tun watan Disambar 2015.

A cewarsu, bai kamata a ci gaba da tsare shi da wasu manyan mabiyansa ba, musamman ganin cewa ba shi da lafiya sakamakon raunin da suke zargin sojoji sun yi masa a lokacin da suka kai farmaki a gidansa da ke Zaria a jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce 'yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar.

Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna 'ya'yan kungiyar na gujewa hayaki mai sa hawaye da 'yan sanda suka watsa musu.

A watan na Disamba ne dai aka yi arangama tsakanin 'yan kungiyar da sojojin Najeriya bayan sojin sun yi zargin cewa 'yan Shi'a sun yi yunkurin halaka shugaban sojin kasa, Laftanar Janar Yusuf Buratai.

Sai dai 'yan kungiyar sun musanta zargin, suna masu cewa sojoji sun kashe dubban mabiyansu.