Masar: Daruruwan 'yan ci-rani sun mutu a jirgin ruwa

'Yan uwan mutanen da suka nutse a jirgin ruwan da ya kife a kogin Barah-Rum

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ana ci gaba da yunkurin ceto 'yan ci-ranin a yayin da 'yan uwansu ke jiran sanarwar hukumomi

Mutanen da suka tsira daga cikin wani jirgin ruwa da ya kife a gabar tekun Masar sun shaida wa BBC cewa daruruwan abokan tafiyarsu ne suka mutu bayan jirgin ya nutse.

Sun ce jirgin dai yana dauke da akalla mutum 550 lokacin da ya kife a kimanin kilomita 12 daga gabar tekun.

Hukumomi sun ceto akalla mutum 163 sannan suka gano gawarwakin mutum 42 a kusa da birnin Rosetta da ke da tashar jiragen ruwa.

Jami'an kasar ta Masar sun ce an kama matuka jirgin hudu a kan zarginsu da hannu wajen kifewarsa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutum 10,000 ne suka mutu a lokacin da suke yunkurin tsallakawa Turai ta kogin Bahar-Rum tun daga shekarar 2014.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

An tsare wasu daga cikin mutanen da aka ceto

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan kasar Masar da Syria da Sudan da Eritrea da kuma Somali na cikin wadanda aka ceto