Amurka: An saka dokar ta-baci a birnin Charlotte

Asalin hoton, Getty Images
An fara zanga-zangar cikin kwanciyar hankali amma daga baya sai rikici ya barke
Hukumomi a jihar North Carolina ta Amurka sun kafa dokar ta-baci a birnin Charlotte, bayan wani rikici ya barke a zangar-zangar da ake yi kan kisan wani bakar fata da 'yan sanda suka yi.
A ranar Talata ne dai wani jami'i bakin fata ya harbe Keith Lamont Scott har lahira.
'Yan sanda sun ce daya daga cikin masu zanga-zangar na cikin wani mummunan hali bayan harbe-harben da aka yi tsakanin fararen hula.
Mista Scott ne bakin mutum na uku da 'yan sandan Amurka suka kashe a mako guda.
Irin wadannan harbe-harbe na haddasa zanga-zanga a kasar.
'Yan sanda a garin Charlotte din sun yi amfani da barkonon tsohuwa a lokacin da suka tunkarin masu zanga-zangar.
'Yan sandan garin sunce jami'ansu hudu sun jikkata.