Amurka: Yaro ya yi wa dan gudun hijira tayin gidansu

Wani yaro dan Amurka ya yi wa dan gundun hijirar Syria gidansu

Asalin hoton, White House

Bayanan hoto,

Alex ya yi tayin ne a wata wasika da ya aike wa Shugaba Obama

A wata wasika da ya rubutawa shugaban Amurka, wani yaro dan kasar Amurka mai shekara 6 ya yiwa wani yaro dan gudun hijiran Syria tayin gidansa.

Wasikar da Alex, wanda ke zaune a birnin New York, ya rubuta ta bazu a duniya.

Alex ya rubuta wasikar ne bayan da ya ga hoton Omran Daqneesh mai jini duk a jikinshi wanda ya ja hankulan mutane da dama a duniya.

Mista Obama ya ce wasikar ta fito ne daga wurin yaron da ba shi da son kai ko zargi ko tsoro.

Mutane sun rarraba bidiyon sama da sau 60,000 a shafin sada zumunta na Facebook.

A wasikar ta Alex da fadar shugaban Amurka ta wallafa, ya ce " Shugaba Obama, ka tuna yaron nan da motar daukar marasa lafiya ta dauke shi a Syria?

Ya kuma kara da cewa " Za ka iya zuwa ka dauko shi ka kawo min shi gidanmu, muna sauraronku da tutoci da filawowi da kuma balanbalan da yawa. Za mu samar mai dangi kuma zai zamo dan uwa na."