Hajj: An gano gawa a jirgin Nigeria mai jigilar alhazai yana mayar da su

An gano gawa a jirgin Nigeria

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

An gano gawa a jirgin Nigeria mai jigilar alhazai yana mayar da su

An gano gawar wani bakar fata a jirgin mahajjatan Nigeria.

An gano gawar ne a lokacinda ake ci gaba da jigilar alhazan Najeriya zuwa gida daga Saudiya bayan aikin hajjin bana.

Hukumar alhazan Najeriya ta tabbatar da rahotanin dake cewa an gano gawar bakar fatan ne a kurumbon tayar wani jirgin sama mai jigilar alhazai yana mayar da su gida.

Alhaji Abdullahi Mukhtar Muhammad shi ne shugaban hukumar alhazai ta Najeriya kuma ya shaidawa BBC cewar, mutumin wanda aka gano gawarshi, ba alhaji bane.

Ya kara da cewa ana bincike a kan gawar domin a tabbatar da ko wane ne inda ya ce ana zaton wani ne da ya shiga kafar jirgin ya buya, jirgin ya tashi da shi ba tare da an sani ba.