China: An dakatar da 'yar jarida saboda ta sanya tabarau

'Yar jaridar ta yi wa ma'aikatan agaji a yankin Xiamen tambayoyi

Asalin hoton, XIAMEN WANGSHI

Bayanan hoto,

Shin a iya cewa 'yar jaridar ta bata aikinta saboda ta sanya tabarau da rike lema?

Wani gidan talabijin na kasar China ya dakatar da wata ma'aikaciyarsa saboda ta sanya tabarau sannan ta rike lema domin maganin rana a lokacin da take yi wa wani tambayoyi.

An dauko hoton 'yar jaridar, wacce ba a fadi sunanta ba, tana yi wa wasu mutane tambayoyi a birnin Xiamen a kan kokarin da ake yi na farfado da birnin bayan mahaukaciyar guguwar da ta auka masa.

Shigar da ta yi ta sha bamban da ta mutanen da take yi wa tambayoyi, lamarin da ya sa aka yi ta tsokaci a kanta cewar abin da ta yi ya sabawa yadda ake aikin jarida.

A wata sanarwa da gidan talabijin na Xiamen ya fitar ya ce: "Daya daga cikin ma'aikatanmu ba ta bi ka'idojin aikin jarida wajen yi wa mutane tambayoyi ba, kuma hakan ya yi mummunan tasiri kan al'uma."

Masu amfani da shafukan sada zumunta na zamani a kasar dai sun bayyana ra'ayoyi kan halayyar 'yar jaridar, inda wasu ke ganin abin da ta yi bai dace ba yayin da wasu ke ganin hukuncin da aka yanke mata ya yi tsauri.

Masana na yanayi sun ce mahaukaciyar guguwar da ta fadawa birnin mai suna Meranti ita ce guguwa mafi girma da ta auku a wannan shekarar.