Majalisar Wakilai za ta yi bincike kan sace $17bn a Nigeria

NNPC ya yi kaurin suna wajen rashawa da cin hanci

Asalin hoton, Bloomberg

Bayanan hoto,

Ana zargin kamfanin NNPC da hannu a cuwa-cuwa

Majalisar wakilan Najeriya za ta gudanar da bincike a kan ko kamfanoni da hukumonin gwamnatin kasar sun sace man fetur din da kudinsa ya kai $17bn.

An gano adadin ne bayan da aka kwatanta alkaluman yawan man da Najeriya ta fitar da wanda aka shigar kasashen da ya kamata a ce an kai man fetur din.

An dai yi satar da ake zargi ne a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan.

Majalisar ta kafa kwamitin da zai binciki akalla kamfanoni 20 da hukumomin gwamnati biyu da kuma 'yan kwangila da gwamnatin Jonathan ta ba su izinin fitar da man fetur.