Rikicin Syria: An kai sabbin hare-hare a Aleppo

Tattaunawar sulhu tsakanin Rasha da Amurka ya ci tura

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Jiragen sama na yaki sun kai sabbin hare-hare a Aleppo

Jiragen yaki sun yi barin wuta a birnin Aleppo, sa'oi bayan gwamnatin Syria ta sanar da wani farmaki domin karbe yankunan da ke karkashin ikon 'yan tawaye.

A cewar wasu masu fafutika, jiragen sama na yaki na kasashen Syria da Rasha suna ta kai hari a kudancin birnin.

Wani mai aikin bayar da agaji ya bayyana abin da ke afkuwa a matsayin "barna mai tsanani".

Gwamnatin Syrai dai ta bukaci mutane da su guje wa wuraren da ke karkashin ikon 'yan tawayen.

Sai dai ya zuwa yanzu Rasha ba ta tabbatar ko tana da hannu a harin ba.

Tattaunawa tsakanin kasashen Rasha da Amurka domin dawo da yarjejeniyar tsagaita wuta ya ci tura.

Kasar Rasha tana goyon bayan gwamnatin Syria, yayin da Amurka kuma ke goyon bayan masu adawa.