Yadda mata ke goya mazansu a wani tsibiri da ke Rwanda

Al'ada ce mazan tsibirin ke so sosai
Bayanan hoto,

Matan tsibirin Nkombo a kasar Rwanda na goya mazansu

Wakilin BBC Yves Bucyana ya gano wata al'adar da ba kasafai ake ganin irinta ba a tsibirin Nkombo da ke yammacin kasar Rwanda.

Wata al'ada ce da mazan da ke zaune a wannan tsibirin suke so sosai.

Wakilin BBC ya ce ba wani sabon abu ba ne mata ta wanke kafar mijinta kuma ta shafa wa kafar mai, sannan kuma ta kinkime shi ta goya shi ta kai shi gado.

Matan da suka yi wa wakilin BBC magana sun ce wannan al'adar ba takura masu ake yi ba, amma alama ce ta nuna soyayyarsu ga mazansu.

A cewar Josephine Nyirantibashima mai shekaru 48, "Da zarar mijinki ya dawo daga wurin aiki, zai zo ya tarar da ruwan dumi, sai ki wanke mashi kafarshi, saboda a lokuta da dama, zai kasance ya dawo a gajiye, sai ki goya shi ki kai shi gado".

Shugabannin addini sun ce al'ada ce da ake bai wa muhimmanci.

"Idan muna bai wa amare da mazansu shawarwari a wannan cocin, suna gaya mana cewa al'adarsu ce. Ba abu ba ne da ake tirsasa wa mata su yi; suna yi ne domin su tsare aurensu",a cewar Fasto Hanyurwa Jean.

Jami'an gwamnati sun ce akwai wahala idan aka ce za a hana wannan al'adar, amma ba sa bayar da kwarin gwiwar aiwatar da ita.